ABNA24 : Da take sanar da hakan, mataimakiyar wakilin dindindin na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Zahra Ershadi, ta ce "Tsawon shekaru da yawa na rashin daukar mataki daga MDD, hakan ya kara karfafawa gwamnatin sahayoniya ci gaba da aikata muggan laifuka a gabas ta tsakiya musamman kan al’ummar Falasdinu.
A daya bangaren kuma jami’ar, ta caccaki Amurka saboda yadda take karfafawa Isra’ila ta hanyar hawa kujerar na ki, game da duk wani kudiri da aka gabatar a kwamitin Tsaron MDD.
Zahra Ershadi, ta kawo misalign, matakin da Amurka ta dauka, a cikin watan Mayun 2021, na hana Kwamitin Tsaro fitar kudiri na kawo karshen harin da Isra'ila ta kai Gaza."
342/